gumelfoundation.org@gmail.com
No. 12, Hadejia Road, Gumel, Jigawa, 732101

GUMEL EMIRATE FOUNDATION

SANARWA DANGANE DA SHIRIN “FOUNDATION YEAR PROGRAM” KARKASHIN “DAN MODI STUDENTS’ CARE”.
Home » Gumel  »  SANARWA DANGANE DA SHIRIN “FOUNDATION YEAR PROGRAM” KARKASHIN “DAN MODI STUDENTS’ CARE”.
SANARWA DANGANE DA SHIRIN “FOUNDATION YEAR PROGRAM” KARKASHIN “DAN MODI STUDENTS’ CARE”.

Kwamatin tantancewar ɗalibai mata masu cin gajiyar shirin "FOUNDATION YEAR PROGRAM", shiri ne wanda gwamnatin jahar Jigawa ta kirkiro dashi ƙarƙashin kungiyar DANMODI STUDENTS CARE, na za ta ɗauki dalibai mata mutum 50 masu sha'awar karatun aikin jinya da ungozomanci a fadin karamar hukumar Gumel da nufin ɗaukar ɗawaniyyar karatunsu daga farko har zuwa kammalawa.

‎Gobe idan Allah ya kaimu Asabar, kwamitin zai sauka a karamar hukumar Gumel, domin gudanar da wannan tantanacewa ga ɗaluban da suka nuna sha'awarsu na tafiya karatun, wannan tantancewa za ta gudana kamar haka:

‎Rana: Asabar 15th November, 2025
‎Wuri: Gumel Emirate Foundation
‎Lokaci: 9:00 na safe

‎ABUBUWAN DA AKE NEMA YAYIN TANTANCEWA:

‎1- Dole sai wacce ta karanta bangaren kimiyya (Science class)
‎2- Dole ta kasance tana da 7-9 credits including (Maths, English, Physics, Biology and Chemistry) a WAEC, NECO ko NABTEB
‎3- Wajibi ne ɗaliba ta kasance tana da shaidar kammala sakandare ɓangaren kimiyya (SCIENCE)
‎4- Wajibi ne ɗaliba ta kasance tana da cikakkiyar shaidar zama yar karamar hukuma (indigine)
‎5- Wajibi ne ɗaliba ta mallaki katin shaidar zama ‘yar ƙasa (NIN) mai ɗauke da bayanan ƙaramar hukuma
‎6- Wajibi ne ɗaliba ta fito daga mazaɓun da suke wajen gari (mazaɓu masu ƙarancin mata likitoci).

‎Allah ta'ala ya bamu sa'a, yasa ayi a kammala lafiya. Sannan ƴan'uwa a taya mu yaɗawa domin kannenmu da yayyenmu mata su kasance cikin shiri kafin goben.

‎09037400265
‎08036261657

Cc: Aliyu Bala Maina
‎Coodinator Gumel LGA - Ɗanmodi Students Care

Signed:
Education Committee
Gumel Emirate Foundation

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *